NE

News Elementor

Sojoji Sun Ceto Mutane 47 Da ISWAP Ta Yi Garkuwa Da Su A Borno

Dakarun Operation Hadin Kai sun ceto mutane 47, mafi yawansu mata da yara, daga hannun mayakan Ƙungiyar Daular Musulunci ta Yammacin Afirka ISWAP a sansanin ƙungiyar da ke Kangarwa, ƙaramar hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

An gudanar da wannan aikin ceto ne a ranar 20 ga Yuni.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Litinin.

Goni ya ce waɗanda aka ceto sun samu ‘yancinsu ne sakamakon ci gaba da hare-haren da sojoji ke kai wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM