NE

News Elementor

NDC ta kori wani ɗan takararta aJihar Borno bisa zargin yiwa Atiku kamfen a zaɓen 2027

Jam’iyyar NDC a jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na majalisar dokokin jihar, Mohammed Bunu, bisa zargin yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, kamfen.

A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 25 ga Oktoba, 2026, jam’iyyar ta ce matakin ya biyo bayan gano wasu kayan kamfe da ke ɗauke da tambarin ADC, hoton Atiku da kuma sunan Bunu.

Mataimakin shugaban NDC na jihar, Umar Fema, ya bayyana cewa an fara binciken ne daga matakin shugabancin mazabar Hausari, kafin a miƙa batun ga shugabancin jam’iyyar na ƙaramar hukumar Maiduguri Metropolitan Council domin zurfafa bincike.

A cewar wasiƙar, an gayyaci Bunu sau biyu, a ranakun 23 da 24 ga Oktoba, domin ya kare kansa kan zargin, amma bai halarci zaman binciken ba.

Bayan nazarin rahoton kwamitin binciken, shugabancin jam’iyyar ya amince da shawarar korarsa, tare da miƙa matakin ga shugabancin NDC na jihar.

Sai dai jam’iyyar ta bayyana cewa batun cire Bunu daga matsayin ɗan takara ya bambanta da batun dakatarwa ko korarsa daga cikakken zama ɗan jam’iyyar, wanda ke buƙatar bin ƙa’idojin kundin tsarin jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM