Rasha ta zargi Faransa da haifar da ta’addanci a nahiyar Africa, tare da ayyana kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi ta Libya a shekarar 2011 a matsayin masomin matsalar.
Moscow ta ce lamarin ne ya fantsama ha rya hadiye dukkanin kasashen Africa, ta hanyar kafuwar kungiyoyin ta’addanci da safarar makamai.
Da take zantawa a wani taron manema labarai, mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakhrova ta ce gwamnatin Paris ba ta yi Nazari kan makomar yankin ba a lokacin da idonta suka rufe har ta kifar da gwmanatin Gaddafi.
Zakharova ta zargi kafafen yada labaran Faransa da yunkurin disashe kokarin da Rasha ke yi wajan yaki da ta’addanci a yankin Sahel, inda ta bukaci kafafen da su yi bincike kna dalilin faruwar rikicin.
Jami’ar diplomasiyyar ta bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na kassara gudummawar Rasha wajan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashen Africa da ke fama da ta’addanci.