
Rikicin ya tashi ne bayan da sojojin suka kashe Nemesio El Mencho, jagoran kungiyar masu safarar ƙwaya ta Jalisco New Generation.
Ƙungiyar na ɗaya daga cikin kungiyoyin da ke haɓaka sosai a ƙasar da ke Arewacin Amirka, yayin da El Mencho ya kasance dilan ƙwaya da ake nema ruwa jallo a ƙasar.
El Mencho ya yi ƙaurin suna wajen safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Amurka, abinda ke sa ana kai wa jami’an gwamnatin da suka kalubalance yan adawa hari.