NE

News Elementor

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani yunƙuri da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka yi na tatsar kuɗin haraji a jihar Yobe

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce bayanan sirri da dakarun suka samu sun nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da wasu motoci da babura wajen tattara kuɗaɗe daga fararen hula a yankin.

Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirrin, dakarunta suka gudanar da sintiri na musamman a yankin Paya Kafiya ranar 19 ga Yulin 2026.

Bayan sun yi arangama da ‘yan ta’addan, sojojin suka buɗe musu wuta, inda suka lalata ɗaya daga cikin motocinsu tare da kashe direban motar.

Rundunar ta ƙara da cewa wasu ‘yan ta’adda huɗu sun tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.

A wani samame da sojojin saka ci gaba da yi ranar 20 ga Yuli, sun yi nasarar ƙwato makammai da harsasai da wata mota..

Rundunar ta ce nasarar ta taimaka wajen tarwatsa hanyoyin samun haramtattun kuɗaɗen Boko Haram/ISWAP a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani yunƙuri da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka yi na tatsar kuɗi daga al’ummomi a Jihar Yobe ta hanyar karɓar haraji ba bisa ka’ida ba.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce bayanan sirri da dakarun suka samu sun nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da wasu motoci da babura wajen tattara kuɗaɗe daga trt hula a yankin.

Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirrin, dakarunta suka gudanar da sintiri na musamman a yankin Paya Kafiya ranar 19 ga Yulin 2026.

Bayan sun yi arangama da ‘yan ta’addan, sojojin suka buɗe musu wuta, inda suka lalata ɗaya daga cikin motocinsu tare da kashe direban motar.

Rundunar ta ƙara da cewa wasu ‘yan ta’adda huɗu sun tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.

A wani samame da sojojin saka ci gaba da yi ranar 20 ga Yuli, sun yi nasarar ƙwato makammai da harsasai da wata mota..

Rundunar ta ce nasarar ta taimaka wajen tarwatsa hanyoyin samun haramtattun kuɗaɗen Boko Haram/ISWAP a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM