NE

News Elementor

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Ceto Wasu Yan Mali 30 Daga Masu Safarar Mutane

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara akan wani gungun masu safarar mutane, dake aikata aika-aika a tsakanin Abuja fadar gwamnatin ƙasar da makoftanta, inda ta ceto wasu ƴan ƙasar Mali 30, sakamakon bayanan sirri da suka samu.

Rundunar ta kai ga ceto ‘yan kasashen wajen 30 tare da kama wasu mutane goma sha uku 13 da ake zargi da alaka da kungiyoyin masu aikata laifuka.

Waɗanda ake zargin dai sun da Abdul Ngaki jagoran tafiyar da Fatima Kulibali da Ahmad Kasango da Sidibe Musa da Muhammed Dembele sai Sa’idu Traore da Ali Koulibali da Abdul Ngeki da dai sauransu.

Rundunar ƴansandan ta ci gaba da cewa wannan nasarar ta biyo bayan wasu bincike da suka gudanar ne da kuma bayayn sirrin da suka samu dangane da bacewar ƴan wasu ƙasashe da ake fuskanta a cikin ƙasar.

Wani bincike da aka gudanar tun daga farko ya nuna cewa kungiyar ta yi wa matasa daga kasashen yammacin Afirka musamman Mali da Gabon romon baka ne da zummar zasu fitar dasu kasahsen Turai da kuma sama musu ayyukan yi mai tsoka a Najeriya.

Gungun masu safarar mutane sun karɓe kuɗaɗen waɗanda abin ya shafa ne da sunan kuɗin ai da sufuri yayin da suka jibge su a wasu gidaje a Mararaba da Karu, da kuma Jihar Nasarawa, inda ake tsare da su a karkashin a cikin mummunan yanayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM