Sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Musa Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa ADC, yana mai danganta matakin da rikicin cikin gida da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a jihar ta Kebbi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Maidoki wanda shine shugaban kwamitin majalisar dattawa kan bibiyar aiwatar da dokoki kuma mataimakin shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kai na majalisar, ya bayyana cewa matsalar cikin gida da ta biyo bayan zaɓen fidda gwani ne ya sa ya sauya sheƙa.
Jaridar ta kuma ce yana cikin waɗanda aka hana shiga takarar zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a da aka gudanar a kwanakin baya.