NE

News Elementor

Shettima Ya Gargadi ‘Yan APC Da su Guji Rarrabuwar Kai Gabanin Zaben Fidda Gwani

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya gargadi magoya bayan jam’iyyar APC da su guji haddasa rarrabuwar kai gabanin zabukan fidda gwani na 2027.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, Shettima ya ce akwai masu neman tayar da fitina da za su iya haddasa rikici a cikin jam’iyyar, yana mai kira ga shugabanni da ‘yan takara da su rungumi hadin kai da juriya.

Ya jaddada cewa jam’iyya ba filin yaki ba ce, illa gida daya da ya kamata a kiyaye.

Ya kuma bukaci a gudanar da zabukan cikin gaskiya da adalci, tare da bai wa ‘yan takara da wakilai damar yin zabi cikin ‘yanci. A cewarsa, nasarar jam’iyya ba za ta tabbata ba sai idan an kasance cikin hadin kai.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa rikice-rikicen cikin gida na iya raunana APC kafin babban zabe, yana mai kira ga kowa da kowa da ya nuna hakuri, ladabi da mutunta juna domin cimma nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM