NE

News Elementor

Shugabannin ƙungiyar Ansaru da gwamnatin Najeriya ke zargi da laifukan ta’addanci sun amsa laifukansu a kotu

An kama mutanen ne tun a shekarar 2025 bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai musu.

Mutanen biyu da ake zargi Mahmud Usman, wanda hukumomi suka ce shi ne jagoran ƙungiyar Ansaru, da kuma Abubakar Abba, wanda ake zargi dan shi ne mataimakinsa sun amsa dukkan tuhume-tuhumen 32 da ake musu.

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyansu Bala Dakum ya shaida wa kotun cewa bayan tattaunawa da waɗanda yake karewa, sun amince da tuhume-tuhumen bayan sake karanto su a gaban kotu,
Hukumar SSS ta gurfanar da su a gaban kotu tun a watan Satumbar 2025 kan tuhume-tuhumen da suka haɗa da ɗaukar nauyin ta’addanci, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ƙera bama-bamai na gida da kuma wasu laifuka masu alaƙa da ta’addanci.

Hukumar ta kuma zarge su da jagorantar ƙungiyoyin ta’addanci a ɓoye, da shirya hare-hare, da kuma alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci masu alaƙa da Al-Qaeda da ke aiki a yankunan Sahel da Maghreb.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM