NE

News Elementor

Sojoji sun ceto fasinjoji 33 da ‘ƴan ta’adda suka yi garkuwa da su

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto fasinjoji 33 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne bayan sojojin haɗin gwiwar Operation FANSAN YAMMA sun samu rahoton sace fasinjojin da ke tafiya ta yankin Magazu a ranar Asabar.

Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Hadin Gwiwar Soji ta Arewa maso Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce sojojin Sector 2 tare da jami’an ’yan sanda da ke Tsafe sun gaggauta isa wurin bayan samun bayanan satar.

Ya ce sojojin sun yi arangama da ’yan ta’addan a lokacin da suke ƙoƙarin tura fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba.

A cewar rundunar, sojojin sun yi musu luguden wuta, lamarin da ya tilasta musu guduwa zuwa cikin daji tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Dakarun sun samu nasarar kubutar da dukkan fasinjoji 33, kuma sun fara farautar ’yan ta’addan da suka tsere domin cafke su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM