NE

News Elementor

Sojoji sun ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su a jihar Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ’yan ta’adda da kuma kama wasu da ake zargi da aikata laifuka yayin samamen da ta gudanar a sassa daban-daban na kasar tsakanin 11 zuwa 17 ga Satumba, 2026.

Daraktan yada labarai na rundunar tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa kan nasarorin da sojojin suka samu.

Ya ce dakarun sun kuma kwato makamai da alburusai, tare da lalata hanyoyin samar da kayan aiki da kuma hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda da masu ba su bayanai. Haka kuma, an gano tare da kwance bama-bamai 12 da aka binne a wurare daban-daban.

A Jihar Neja, dakarun Operation Savannah Shield sun ceto mutane 22 da aka yi garkuwa da su a kauyen Muchiya da ke karamar hukumar Rafi, yayin da suka kashe ’yan ta’adda biyar a ayyuka daban-daban a Neja da Kwara.

A Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun ceto mutane 14 a yankin Gwoza na Jihar Borno, ciki har da babban limamin Ngoshe, Malam Sadiq, wanda aka sace a watan Maris.

Rundunar ta ce ta kuma ceto wata mata da ta shafe watanni biyar a hannun ’yan ta’adda da wasu yara biyu da suka kwashe watanni shida a zaman talala.

A Arewa maso Yamma kuma, Operation Fansan Yamma ta ceto wasu mutanen da aka sace a Katsina, Kaduna da Sokoto, ciki har da mutane 10 a kauyen Unguwan Rimi da ke Sabuwa, Katsina.

A yankin Arewa ta Tsakiya, sojojin Operation Whirl Stroke sun kama wasu da ake zargi da kasancewa masu ba ’yan ta’adda bayanai da kuma masu samar musu da kayayyaki a Benue, Kogi da Taraba.

A Kudu maso Gabas, Operation UDO KA ta lalata wata matatar mai ba bisa ka’ida ba a Imo, inda ta lalata kusan lita 1,300 na danyen man da aka sace. Haka kuma, an kama wani da ake zargi da kera bama-bamai ga wata kungiyar ’yan aware.

A Edo kuwa, Operation Delta Safe ta kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane, tare da kwato bindigar AK-47 da alburusai.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa sojojin bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi, tare da kira ga al’umma da shugabannin gargajiya su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM