Dakarun Rundunar Sojin Najeriya da ke karkashin Sashe na 2 na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun dakile yunkurin sace mutane da dama tare da ceto Shugaban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda, Dr. Aminu Yusuf, da wasu mutane da dama a wasu hare-hare daban-daban da suka faru a jihar Zamfara.
Rundunar sojin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya wallafa a shafinsa na X.Sanarwar ta ce lamarin na farko ya faru ne da sanyin safiyar ranar 28 ga Yuli, lokacin da dakarun suka amsa kiran gaggawa bayan samun rahoton cewa ‘yan ta’adda na kai hari a yankin Tsohon-Tasha Street da ke karamar hukumar Kaura Namoda.
Aliyu Danja ya ce maharan sun kutsa cikin gidan shugaban kwalejin, inda suka kashe jami’in tsaronsa mai zaman kansa, suka kuma jikkata wani mazaunin gidan kafin su yi yunkurin yin garkuwa da Dr. Yusuf da wasu daga cikin iyalansa.
Kakakin rundunar ya kara da cewa, a wani samame daban da aka gudanar a wannan rana, dakarun da ke sintiri da daddare sun amsa wani kiran gaggawa daga al’ummar Tungan Dorawa da ke kauyen Barkeji, inda ‘yan ta’adda ke kokarin yin garkuwa da mazauna yankin.
Ya ce duk da cewa yanayin hanyar ya jinkirta isar dakarun da farko, daga bisani sun bi sawun wadanda ake zargin, suka fafata da su, tare da dakile yunkurin yin garkuwa da mutanen.