NE

News Elementor

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 1,106 a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai ta ce ta hallaka ’yan ta’adda 1,106 na Boko Haram da ISWAP, tare da cafke sama da naira miliyan 300 da aka samu daga haramtattun kudade na masu daukar nauyin ’yan ta’addan.

Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai mai barin gado, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin jawabinsa na bankwana da aka gudanar a Maimalari Cantonment da ke Maiduguri, Jihar Borno.

A cewar kwamandan mai barin gadon, wasu manyan hare-haren soji da aka gudanar sun kuma kai ga cafke akalla mutane 758 da ke taimakawa kungiyoyin ’yan ta’addan wajen samar musu da kayayyakin aiki da sauran bukatu.

Ya danganta nasarorin da aka samu a ayyukan sojin da hadin gwiwar matsin lamba na soji da ake ci gaba da yi, tare da ingantattun hanyoyin tattaunawa da sauran matakan da ba na amfani da karfin soji ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM