NE

News Elementor

Sojoji Sun Kashe Na Hannun Daman Bello Turji

Rundunar Sojin Najeriya ta Division 8 ta kashe wani fitaccen kwamandan ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a Karamar Hukumar Sabon Birni dake Jihar Sokoto.

Wata majiyar tsaro, ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Talata, Inda rundunar ta bayyana hakan a matsayin babban nasara a yakin da take ci gaba da yi da ta’addanci a Arewa maso Yamma.

Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa Kallamu, wanda ya kasance amintacce kuma daya daga cikin hannun daman shugaban ’yan ta’adda Bello Turji ne, ya gamu da ajalisa a wani gagarumin samame da dakarun Division ta 8 suka kaddamar tare da hadin gwiwar yan banga na yankin.

Rahoton ya ce an hallaka Kallamu tare da daya daga cikin manyan masu samar wa Turji kayayyaki a daren Litinin, yayin wani farmaki da sojojin suka kai kauyen Kurawa.

Dan ta’adda Kallamu, dan asalin Garin-Idi a yankin Sabon Birni ne, wanda ya dade yana addabar al’ummomin shiyyar gabashin Sakkwato, inda hare-harensa suka tilastawa jama’a barin gidajensu tare da haifar da tsananin tsoro da furgici.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM