Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sake komawarsa kan mulki a zaɓen 2027 a jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoba, kamar yadda daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana.
Yari ya bayyana hakan ne ranar Juma’a bayan ganawa da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen.
Ya ce za a gudanar da taron farko na kwamitin yaƙin neman zaɓen ranar 14 ga Oktoba a fadar shugaban ƙasa, kafin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Kaduna.
A cewarsa, bayan Kaduna, tawagar za ta wuce Fatakwal ta jihar Rivers, sannan ta je Maiduguri ta jihar Borno.
Yari ya kuma yi watsi da yiwuwar ‘yan adawa su kayar da Tinubu, yana mai cewa samun goyon baya daga jihohin Arewa da Kudu na da muhimmanci wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Ya yi iƙirarin cewa Tinubu na da goyon baya a fiye da jihohi 10 a Arewa da kuma fiye da 10 a Kudu.
Haka kuma, Yari ya kare ayyukan gwamnatin Tinubu, yana mai cewa tattalin arzikin ƙasar na samun sauyi.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 16 ga Janairu, 2027 a matsayin ranar zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya.