Tsohon Shugaban Sashen Harkokin Kuɗaɗe na Kamfanin NNPCL, Alhaji Umar Ajiya, ya ƙaryata zargin da Kwamitin Majalisar Dattijai kan Asusun Kuɗaɗen Gwamnati ya yi wa tsohon Shugaban Kamfanin, Mele Kolo Kyari, na ɓatan naira tiriliyan 210 daga kamfanin tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023 a lokacin da suke jagorantar harkokin kamfanin.
Shugaban Ƙungiyar Ajiya Solidarity Forum, Comrade Usman Abubakar, a wata tattaunawa da ya yi da Hausa Daily Times da kuma tashar NTA Sokoto, a madadin Ajiya.
Idan ba a manta ba, a makwannin baya ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai kan Asusun Kuɗaɗen Gwamnati, Sanata Ahmad Aliyu Wadada, ya sanar da tura sammaci tsoffin manyan jami’an kamfanin albarkatun mai na Najeriya NNPCL a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, domin su bayyana a gaban kwamitin don amsa tambayoyi dangane da zargin ɓatan waɗannan kuɗaɗe.
Sai dai Shugaban Ƙungiyar Ajiya Solidarity Forum, ya bayyana zargin a matsayin wanda “hankali ba zai karɓa ba”. Ya ce adadin kuɗaɗen da kwamitin ya ce sun ɓata ya yi matuƙar yawan da ba za a ce ba a gane ɓatansu ba tsawon wannan lokaci, domin yawansu zai iya aiwatar da kasafin kuɗin Najeriya na shekaru.
Usman ya bayyana cewa Alhaji Umar Ajiya a shirye yake ya amsa gayyatar kwamitin a matsayinsa na tsohon babban jami’in da ke kula da harkokin kuɗaɗen kamfanin, domin ya wanke kansa daga zargin da ya kira mara tushe, yana mai cewa akwai hujjoji da dama da zai gabatar.
Ya kuma jaddada cewa babu ƙanshin gaskiya a zargin da ake yi wa Ajiya da Mele Kyari na ɓata kuɗaɗen kamfanin a lokacin da suke jagorantar NNPCL.
Sai dai ya yi zargin cewa shugaban kwamitin, Sanata Ahmad Aliyu Wadada, ya bijiro da wannan batu ne saboda rashin samun cin hancin dala dubu ɗari biyar ($500,000) da ya taɓa nema a hannun Ajiya.
Usman Abubakar a madadin Ajiya, ya buƙaci al’ummar Najeriya da su yi watsi da zargin da kwamitin ya yi.
Daga ƙarshe ya tabbatar da cewa Ajiya a shirye yake ya bayyana wa duniya shaidar cin hanci da Wadada ya nema a wurinsa. Sannan zai baiwa duk wata hukuma da ta shirya yin bincike kan wannan zargi haɗin kai domin gaskiya ta yi halinta.