Shugaban kasa Bola Tinubu ya jaddada kudurinsa na dorewar dimukradiyya da doka da oda a Nigeria, a matsayin abubuwan da zai bari domin a rinka tunawa da shi.
Ya ce hadin kai da ci-gaban kasa sun dogara ne kan kyakkyawan shugabanci, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kiyaye wadannan abubuwan domin samun nasara a rayuwa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a liyafar buda-baki da ya shiryawa shugabannin jamiyyar APC, da na majalisar hadin-kan jamiyyu ta kasa, IPAC, a fadarsa dake Abuja.
Ya ce karfafa tsarin dimukradiyya a cikin jamiyyu babban ginshiki ne da zai samar inganta sha’anin zabe a kasar nan.
Shugaba Tinubu ya ci-gaba da cewa, amfani da tsarin kato-bayan-kato wajan fitar da yan takara zai ba wakillan jamiyyu damar fafatawa a harkokin da suka shafi tsayar da yan takara a dukkan mukaman gwamnati.