An rantsar da tsohuwar jarumar fina-finan batsa, Deyci Alejandra Omaña Ortiz, wadda aka fi sani da Amaranta Hank, a matsayin sanata a ƙasar Colombia bayan ta lashe zaɓen da aka gudanar a watan Maris.
Ortiz za ta wakilci yankin Norte de Santander a majalisar dattawan ƙasar a ƙarƙashin jam’iyyar Historic Pact na wa’adin 2026 zuwa 2030.
Ta ce tarihin rayuwarta bai kamata ya hana ta yin hidima ga al’umma ba, tana mai jaddada cewa ma’aikatan masana’antar nishaɗin manya suna da gudunmawa ga tattalin arzikin ƙasa kuma sun cancanci kariya da amincewa a ƙarƙashin doka.
Sabuwar sanatan ta kuma bayyana cewa za ta mayar da hankali kan batutuwan lafiyar ƙwaƙwalwa da yaƙi da cin zarafi ta hanyar jima’i, duk da suka da ce-ce-ku-cen da naɗinta ya haifar a fagen siyasar Colombia.