NE

News Elementor

Wani sanatan Amurka makusancin Trump ya rasu

Sanata mai wakiltar jam’iyyar Republican daga jihar South Carolina a Amurka, Lindsey Graham, ya rasu yana da shekaru 71 bayan wata gajeriyar jinya.

Ofishinsa ne ya sanar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da aka fitar da yammacin ranar Asabar.

Graham ya shafe fiye da shekaru ashirin yana aiki a Majalisar Dattawan Amurka, inda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan Republican kuma aminin shugaban ƙasar Amurka Donald Trump.

Marigayin ya yi fice saboda tsattsauran ra’ayinsa kan manufofin harkokin waje, musamman game da Iran.

Ya kasance mai goyon bayan matakan matsin lamba kan Tehran, ciki har da ƙaƙaba ƙarin takunkumai da kuma ɗaukar matakai masu tsauri kan shirin nukiliyar ƙasar da ayyukanta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM