Tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche (mai ritaya), ya yi kira da a sake duba jin daɗi da walwala sojojin Najeriya, inda ya ba da shawarar cewa a riƙa biyan sojojin da ke da ƙananan mukamai albashin aƙalla ₦250,000 a kowane wata, domin ya dace da halin tsadar rayuwa da kuma irin nauyin aikin soja.
Enenche, wanda kuma ƙwararren masanin dabarun soja ne, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da ARISE TV a ranar Lahadi.
Da aka tambaye shi dalilin wannan shawara, tsohon Janar ɗin ya ce wannan adadi ƙaramin misali ne idan aka yi la’akari da yadda tsadar rayuwa ke ƙaruwa a ƙasar da kuma irin sadaukarwar da aikin soja ke buƙata.