Wani babban jami’in kula da harkokin kuɗi na ƙungiyar ISWAP tare da yara maza biyu sun miƙa wuya ga dakarun Bataliya ta 3 ƙarƙashin Rundunar Task Force Brigade ta 24 ta Operation Hadin Kai a Jihar Borno.
Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Asabar, tana mai bayyana lamarin a matsayin wani gagarumin nasara da aka samu a yaƙin da ake yi da ta’addanci.
Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce mutumin ya miƙa wuya da misalin ƙarfe 6:45 na safiyar ranar 25 ga Yuli, 2026, a kan hanyar Ladari–Jegarawa–Tunokalia da ke kan babban titin Gamboru–Wulgo a Jihar Borno.
Ya ce wannan nasara na nuna tasirin hare-haren ƙasa da na sama da kuma bayanan sirri da rundunar ke amfani da su wajen murƙushe ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun ƙarin mika wuya daga ‘yan ta’adda, inda kusan ‘yan ta’adda 46 tare da iyalansu suka miƙa wuya ga sojoji cikin ‘yan kwanakin nan.
Kyaftin Goni ya ce binciken farko ya nuna cewa mutumin shi ne babban jami’in kula da harkokin kuɗi na sansanin ISWAP da ke Jubillaram, inda yake da alhakin tafiyar da kuɗaɗe da kuma kayan aiki na ƙungiyar.
An ce ya miƙa wuya tare da yara maza biyu, yayin da aka ƙwato daga hannunsa bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, magazin huɗu, harsasai 101 na 7.62mm, babur guda ɗaya da kuma kuɗi Naira 40,000.
Rundunar sojin ta ce ana ci gaba da yi masa tambayoyi da tantancewa domin samun bayanan sirri da za su taimaka wajen ci gaba da farmakar sauran ‘yan ta’addan da ke yankin.
Ta ƙara da cewa mika wuya da wannan babban jami’in kula da kuɗaɗen ISWAP ya yi babbar illa ce ga tsarin gudanarwar ƙungiyar, kuma hakan na nuna cewa hare-haren Operation Hadin Kai na ci gaba da raunana ƙarfin ISWAP da hanyoyin samun kuɗaɗenta.