Wata ƙungiyar wayar da kan jama’a kan siyasa mai suna Da Hannu Na, ƙarƙashin dandalin Arewa for Asiwaju, ta isa Jihar Bauchi domin lallashin Gwamna Bala Mohammed ya goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Haka kuma, ƙungiyar ta bayyana shirin ziyartar gidan gyaran hali domin tallafa wa fursunoni, ciki har da biyan tarar waɗanda suka cancanci samun ’yanci, waɗanda adadinsu ya haura 150.
Shugaban ƙungiyar, Jamilu Jadda Garko, ne ke jagorantar wannan shiri, wanda a cewar ƙungiyar ke da nufin samar da hanyar tattaunawa tsakanin Gwamna Bala Mohammed da Shugaba Tinubu.
Ƙungiyar ta ce tana son ƙarfafa tattaunawar siyasa, haɗin kai da kuma gano abubuwan da shugabannin biyu za su iya cimmawa tare gabanin babban zaɓen 2027.
A yayin ziyarar, ƙungiyar ta kuma shirya ganawa da malaman addinin Musulunci da malaman makarantun Tsangaya domin tattauna batutuwan da suka shafi ilimin addini da bunƙasa al’umma.
Dangane da shirin tallafa wa fursunoni, ƙungiyar ta ce za ta kai musu ziyara tare da ba su kyaututtuka, sannan ta biya tarar waɗanda suka cancanci a sake su bisa tanadin doka.
Ta bayyana cewa shirin zai shafi sama da fursunoni 150 da ke da shari’o’in farar hula. Sai dai ba a bayyana jimillar kuɗin da ake buƙata domin biyan tarar ko cikakken tsarin sakin waɗanda abin ya shafa ba.
Ƙungiyar ta ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen jin ƙai da take aiwatarwa domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da mutanen da matsalolin kuɗi suka jefa cikin ƙunci.
A ɓangaren siyasa kuwa, Da Hannu Na ta ce ziyarar Bauchi wani ɓangare ne na dabarunta na tuntuɓar masu ruwa da tsaki da gina alaƙa tsakanin jam’iyyu daban-daban gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta nuna fatan cewa tattaunawar da take son yi tsakanin Bala Mohammed da Tinubu za ta iya yin tasiri ga siyasar Jihar Bauchi.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da matsayin Gwamna Bala Mohammed kan wannan yunƙuri ba, kuma babu wata sanarwa da ke nuna cewa ya amince zai goyi bayan Tinubu sakamakon shiga tsakani da ƙungiyar ke shirin yi.
Baya ga harkokin siyasa, ƙungiyar ta ce tana gudanar da ayyukan addini a jihohi 13 na ƙasar, inda take hulɗa da kusan makarantun Islamiyya da Tsangaya 300.