NE

News Elementor

Yadda Matsalar Tsaro Ke gurgunta Kiwon Lafiya a Zamfara

Daga: Shehu Muhammad Shehu

Matsalar tsaro ta jefa al’ummar Zugu da ke karamar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara cikin rashin tabbas, yayin da mazauna yankin ke shan baƙar wahala wajen samun muhimman ayyukan lafiya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto da Nigeria Health Watch ta wallafa, wanda ya yi bayani kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da gurgunta ayyukan kula da lafiyar matakin farko a yankin.

Rahoton ya nuna cewa yawan hare-haren yan bindiga sun tarwatsa harkokin noma da kasuwanci, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin talauci da toshe masu hanyoyin samun abinci, tare kashe kuɗi masu yawa wajen bin hanya mai haɗari domin neman kulawar likitoci.

Jihar Zamfara, wadda tana daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da suka fi fama da matsalar hare-haren yan ta’adda da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa, na fuskantar tarin kalubale a fannin kulawa da lafiyar jama’a a kauyuka irin su Zugu.

A cewar rahoton, Yawancin mazauna yankin, idan mutum na neman magani, a yanzu dole ne sai ya yi tafiya mai tsawo sa ke tattare da haɗari.

Nigerian Health Watch ta ruwaito yadda, a watan Nuwamban 2025, dole ta sa wata mata mai suna Sadiya Abdullahi mai shekara 35 da ke da ‘ya’ya uku a garin Zugu zuwa wata cibiyar shan magani a garin bayan yaronta ya kamu da rashin lafiya, saboda cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Zugu wato PHC ta daina aiki.

To sai dai duk da maganin da aka ba ta bai warke ba, hakan ya cilasta mata yin tafiyar fiye da kilomita 30 zuwa Babban Asibitin Gummi a hanyoyin daji masu haɗari, wadanda ake ganin ba su da tsaro sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.

Halin da ake ciki a Zugu ya wuce kalubalen tsaro kawai.

Rahoton ya bayyana shi a matsayin rushewar tsarin kula da lafiya a matakin farko, inda rufe cibiyoyin kula da lafiya suka mayar da bukatun jinya na yau da kullum zuwa tafiye-tafiye masu barazana ga rayuwa, lamarin da ke haddasa jinkirin kai marasa lafiya asibiti da kuma mace-macen mata masu juna biyu da jarirai da za a iya kaucewa.Mata masu juna biyu na daga cikin wadanda abin ya fi shafa.

Nigerian Health Watch ta ruwaito cewa da dama na haihuwa a gida saboda cibiyoyin da ke kusa da su ko dai an rufe su ko kuma ba sa iya bayar da muhimman abubuwan da ake bukata idan haihuwa ta taso.Haka kuma, samun kulawar kafin haihuwa ya samu tangarda sosai.

Hakimin garin Zugu, Malam Surajo ya ce ayyukan kiwon lafiya sun durƙushe a yankin na tsawon shekaru, amma sun ƙara tabarbare ne bayan manyan hare-haren da aka kai wa garin a shekarar 2023.

Ya ci gaba da cewa, tun daga lokacin, an bar wasu kauyuka babu kowa, yayin da wasu kuma ke rayuwa babu hanyoyin sadarwa da cibiyoyin lafiya.

Rahoton ya ci gaba da cewa mazauna yankin na daukar marasa lafiya cikin gaggawa a kan babura ta hanyoyin daji domin kai su neman magani a garuruwa makwabta kamar Gadar Zaima, Daki Takwas, Maga, Gummi da Bukkuyum.

A baya-bayan nan, an ba da rahoton wata mata mai juna biyu daga kauyen Kairu, wadda ta rasu kan hanyar zuwa asibiti, abin da ke nuna illar rashin samun cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko masu aiki yadda ya kamata.

Jami’in da ke kula da asibitin Zugu, wanda ya shafe sama da shekaru 15 yana aiki a cibiyar, ya ce, a da, cibiyar na samar da ayyukan lafiya ga kauyuka sama da 50 da ke kewaye da yankin.

To sai dai s yanzu, cibiyar na cikin mawuyacin hali, rufin dakuna ya lalace, kofofi da tagogi sun karye, yayin da dakunan kwantar da marasa lafiya ba su da gadaje.Sannan ɗakunan magunguna sun zama babu komai, sai kayan gwajin zazzabin cizon sauro.

Yawaitar hare-hare da barazana sun tilasta wa ma’aikatan lafiya da dama daina zuwa aiki, lamarin da ya janyo raguwar yawan marasa lafiyar da ke zuwa jinya.A kauyen Balhe, mazauna yankin ba sa iya zuwa Zugu saboda matsalar tsaro a kan hanya.

Shugabannin yankin sun kiyasta cewa tsakanin mutane 600 zuwa 700 da ke rayuwa a yankin ba su da damar samun zuwa kowace cibiyar kula da lafiya.Haka kuma, allurar rigakafi ta yau da kullum ta samu tangarda.

Rashin tsaro da tsadar sufuri kan janyo jinkiri ko hana zuwa asibiti, lamarin da ke kara hadarin rasa allurar rigakafi ga ƙananan yara.

Rahoton ya bukaci Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Jihar Zamfara da ta tabbatar da an ɗauki matakan da suka dace da yanayin cibiyoyin kula da lafiya da ke yankunan da ke fama rikice-rikice, ciki har da kula da mata masu juna biyu, allurar rigakafi ta yau da kullum, ganowa da maganin zazzabin cizon sauro, da kuma ingantaccen tsarin tura marasa lafiya.

Haka kuma, rahoton ya bukaci gwamnatin jihar Zamfara da ta tarayya da su dauki matakan kula da lafiya na tabbatar da tsaro, ciki har da taswirar wuraren da ke da hadari, tsara hanyoyin tsaro tare da hadin gwiwar al’ummar yankin, daukar ma’aikatan lafiya yan asalin yankin tare da ba su karin alawus-alawus da tabbatar da ana samar da isassun magunguna da allurai, da samar da motocin da za su riƙa ɗaukar marasa lafiya cikin gaggawa.

Rahoton ya kuma yi gargadin cewa muddin ba a farfaɗo da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a yankunan da ke fama da rashin tsaro ba, rukunin al’umma masu rauni, musamman mata da jarirai, za su ci gaba da shan baƙar wahalai, lamarin da ke kawo cikas ga kokarin cimma cikakken tsarin kiwon lafiya ga kowa a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM