NE

News Elementor

’Yan Bindiga Sun Sace Mutum 5 Da Mata 2 Masu Ciki A Wani Sabon Hari A Sakkwato

Maharan sun shiga gida-gida inda a nan ne suka sace mutum biyar a ƙauyen.

Aƙalla mutum biyar, ciki har da mata biyu masu juna biyu ’yan bindiga suka sace a ƙauyen Maiwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a jahar sokoto

Wani mazaunin ƙauyen ya ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 5:10 na yammacin ranar Asabar, ɗauke da makamai a kan babura guda bakwai.

Ya ce sun isa lokacin da wasu mutane ke zaune a masallaci, inda suka harba bindiga sama domin tsoratar da jama’a.

Daga nan ne ’yan bindigar suka shiga gidaje suka yi awon gaba da mutane.

An bayyana sunayen waɗanda aka sace da Sadiya Umar, Firdausi Umar, Maryam Musa, Ubaida Musa da Harira Nura.

Daga cikinsu, Sadiya Umar da Ubaida Musa na da juna biyu kuma suna daf da haihuwa.

’Yan bindigar sun kuma kwashe shanu 12 amma daga baya suka dawo da su.

Sun kuma doke wani mutum mai suna Malam Ya’u, wanda yanzu haka ake kula da shi a asibitin Sabon Birni.

Bayan harin, mazauna ƙauyen da dama sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar, amma sun dawo da safiyar ranar Lahadi.

Mazauna yankin sun buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana irin waɗannan hare-hare aukuwa a nan gaba.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai, bai yi nasara ba domin bai amsa kira ko saƙon da aka aike masa ba har zuwa lokacin ha5da wannan rahoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM