NE

News Elementor

’Yan sanda sun gana da jam’iyyun siyasa a Sokoto kan yakin neman zabe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta gana da shugabannin jam’iyyun siyasa da zababbun shugabannin kananan hukumomi domin tattauna kalubalen tsaro gabanin fara yakin neman zabe da kuma zabukan da ke tafe a jihar.

An gudanar da tarukan daban-daban a hedikwatar rundunar ranar Laraba, inda suka hada da jami’an ’yan sanda masu kula da sassa wato (DPOs), manyan jami’an ’yan sanda da wakilan jam’iyyun siyasa.

Kwamishinan ’Yan Sanda, Hayatu Shaffa, ya ce an shirya tarukan ne domin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, ’yan siyasa da hukumomin kananan hukumomi, don tabbatar da gudanar da yakin neman zabe da zabuka cikin lumana.

A wata ganawa ta daban da aka yi da jam’iyyun siyasa, kwamishinan ya gargadi ’yan siyasa kan yin kalamai ko shiga ayyukan da za su iya kara dagula matsalar tsaro a jihar.

Ya bukaci jam’iyyun siyasa su gudanar da yakin neman zabensu cikin lumana, su mutunta dokokin da ke jagorantar tsarin zabe, sannan su guji duk wani mataki da zai iya haifar da tashin hankali ko barazana ga tsaron jama’a.

Shaffa ya kuma yi kira ga jam’iyyun da su hada kai da ’yan sanda ta hanyar bayar da bayanai cikin lokaci game da barazanar da ka iya tasowa, tare da tabbatar da cewa magoya bayansu ba za su shiga tashin hankali, tsoratarwa ko wasu ayyukan da za su iya kawo cikas ga zabuka ba.

Ya ce ’yan sanda za su ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samar da yanayin tsaro mai kyau da zai ba da damar gudanar da harkokin siyasa, yana mai jaddada cewa tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabuka alhakin dukkan masu ruwa da tsaki ne.

Kwamishinan ya kara yin kira ga shugabannin kananan hukumomi da su tallafa wa hukumomin tsaro a yankunansu, musamman ta hanyar cudanya da al’umma, tattara bayanan sirri da kuma gano masu aikata laifuka.

Kwamishinan ’yan sandan ya bukaci shugabannin kananan hukumomi da su duba cikin al’ummominsu tare da yin aiki da su domin gano mutanen da ke tallafa wa ayyukan miyagun laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM