Ɗan takarar jam’iyyar ADC a kujerar gwamnan Jihar Sokoto, Hon. Manir Muhammad Dan’Iya, ya goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027, Alhaji Atiku Abubakar, kan shirin da ya yi na sake buɗe iyakokin Najeriya na ƙasa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
Dan’Iya ya ce wannan mataki zai farfaɗo da halastaccen cinikayyar ƙetare iyaka, inganta rayuwar jama’a tare da rage tsananin matsin tattalin arziki, musamman ga al’ummomin Jihar Sokoto da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi, Dan’Iya ya ce al’ummomin da ke zaune a kan iyaka sun daɗe suna dogaro da halastaccen ciniki da zirga-zirga tsakanin Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.
Ya ce sake buɗe iyakokin tare da ingantaccen tsarin kula da kwastam, shige da fice da tsaro zai taimaka wajen rage wa ’yan kasuwa, manoma, masu sufuri da ƙananan ’yan kasuwa matsaloli.
Dan’Iya ya kuma danganta farfaɗowar tattalin arziki da inganta tsaro, inda ya ce ƙasar ba za ta samu ɗorewar ci gaba ba matuƙar rashin tsaro na ci gaba da kawo cikas ga harkokin tattalin arziki.
Ya ce ƙara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma na buƙatar amfani da dabarun da suka dogara da bayanan sirri, ƙarfafa kula da iyakoki, inganta aikin ’yan sanda da ƙarfin sojoji, ƙara haɗin gwiwa da al’umma, tare da ɗaukar matakan da za su tarwatsa hanyoyin tallafa wa ƙungiyoyin masu aikata laifuka.