NE

News Elementor

Wani Kwamishina ya yi barazanar cire yatsar duk wanda ya zaɓi wata jam’iyya da ba APC ba a Borno

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Borno, Sainna Buba, ya tayar da hazo, bayan ya yi barazanar cire yatsar duk wani dan adawa da ya zabi wata jamiyya ba APC ba.

Buba ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kungiyar City Boy Movement, wacce ke goyon bayan tazarcen shugaban kasa Bola Tinubu a 2027.

Da yake gabatar da jawabi ga mahalarta taron, kwamishinan ya gargadi yan adawa da masu sukar gwamnati, inda ya yi amfani da kalamai masu nauyi.

Baya ga barazanar illatawa, Buba ya kuma bayyana wani shiri da gwamnati za ta bullo da shi, wanda ya ce zai shafi iya wadanda suka zabe ta ne.Tuni kalaman na Buba suka tayar da hazo, inda alumma ke diga ayar tambaya kan yanayin siyasar jihar Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM