NE

News Elementor

Ƴan daba sun kai wa ƴan jarida hari bayan gangamin APC a Kano

Wasu ƴan jarida da ke aikin ɗaukar rahoto kan wani gangamin jam’iyyar APC a Kano sun fuskanci hari daga wasu da ake zargin ’yan daba ne.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar a bayan harabar City Campus ta Jami’ar North West da ke Kofar Nassarawa, yayin da ’yan jaridar ke kan hanyarsu ta komawa ofis bayan kammala gangamin.

Rahotanni sun ce maharan sun farfasa gilashin bayan wata motar Radio Nigeria da ke ɗauke da ’yan jaridar, tare da lalata wasu sassan motar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, wani ɗan jarida mai aiki da Pyramid FM Kano, Yakubu Abubakar Gwagwarwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce motar na ɗauke da ’yan jarida biyar da ’yan sanda uku.

Ya ce maharan suna ɗauke da adduna da wuƙaƙe, kuma sun ci gaba da dukan motar duk da kasancewar jami’an tsaro a cikinta.

Gwagwarwa ya ce direban motar ya samu rauni, yayin da wasu daga cikin ’yan jaridar suka ji rauni sakamakon gutsattsarin gilashin motar.

Sai dai ya bayyana cewa ba su da tabbacin ko harin an kai shi ne kai tsaye kan ’yan jaridar, yana mai cewa wataƙila harin ya kasance na bazata, domin ana iya samun wasu da aka kai wa hari a yankin.

Lamarin ya faru ne bayan APC ta gudanar da wani gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, tare da karɓar wasu fitattun ’yan siyasa da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Wannan ba shi ne karon farko da ake zargin ’yan daba da kai hare-hare yayin harkokin siyasa a Kano ba.

A ’yan watannin da suka gabata, an rawaito cewa akalla mutane uku sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da ake zargin ’yan daba masu alaƙa da siyasa ne suka kai a ranar rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar.

Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM