Ƙungiyoyin Mata Media Organisation da Mata Media Foundation sun yi kira da a ƙara mayar da hankali kan lafiyar kwakwalwa da jin daɗin mata ’yan jarida, bayan gudanar da wani bincike na farko da ya shafi mata ’yan jarida 58 a faɗin Arewacin Najeriya.
Binciken mai taken “Nauyin da Ba a Bayyanawa, Ƙarfin da Ake Rabawa: Fahimtar Lafiyar Kwakwalwa, Ƙyama da Tsarin Kulawa a Tsakanin Mata ’Yan Jarida a Arewacin Najeriya”, ya duba matsin lambar da ya shafi aiki, yanayin jin daɗi a zuciya, hanyoyin samun tallafi da kuma samar da tsarin kula da ma’aikata a ɗakunan labarai.
Daga cikin mata ’yan jarida 58 da suka amsa tambayoyin binciken, Kashi 91 cikin 100 suna fuskantar matsin lambar aiki a wasu lokuta.
Kashi 78 cikin 100 kuma suna fuskantar gajiya da damuwa sakamakon aiki da yawa.
Kashi 86 cikin 100 suna fuskantar gajiya sakamakon yawan aiki ko kuma cunkoson bayanai fiye da yadda za su iya sarrafa su.
Kashi 50 cikin 100, wato mutum 29, sun taɓa yin tunanin barin aikin jarida saboda tasirin da yake yi kan lafiyarsu da jin daɗinsu.
Manyan abubuwan da ke jawo matsin lamba sun haɗa da yin aiki na tsawon sa’o’i da kuma lokutan da ba su da tsayayyen tsari, wa’adin kammala ayyuka, ƙarancin albashi da rashin tabbas na kuɗi, rashin tabbacin ci gaba da aiki, matsin lambar da ke tattare da daidaita aiki da kula da iyali, nuna wariya ta jinsi, rashin kyakkyawar alaƙa a wurin aiki da kuma tasirin ɗaukar rahotannin abubuwan da ke jawo raɗaɗi ko tashin hankali.
Kashi 86 cikin 100, wato mutum 50 daga cikin waɗanda suka amsa tambayoyi, sun bayyana cewa ko dai ɗakunan labaran da suke aiki a cikinsu ba sa samar da tallafin lafiyar kwakwalwa da jin daɗin ma’aikata, ko kuma ba su da tabbacin ko akwai irin wannan tallafi.
Yawancin waɗanda suka amsa tambayoyin binciken sun ce suna dogaro da iyalansu, ma’aurata ko abokan zamansu, abokai, abokan aiki, addu’a, ayyukan ibada, hutawa da kuma nisantar aiki domin samun tallafi da kula da lafiyar tunaninsu.