Rahotannai sun ce akwai yiyuwar masu bukatar siyen mai a farashi mai rahusa daga gidajen man NNPCL, sai sun sauke manhajar kamfanin a wayoyinsu na salula domin neman siyen man da kuma biyan kudi a can.
Bayanan da jaridar Punch ta tattara sun tabbatar da cewa, ba za a rinka siyar da man a farashi mai rahusa ba kai tsaye a gidajen man na NNPC.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da NNPC ta tsawaita wa’adin ragin naira 66 kan kowane lita har zuwa 31 ga watan Oktoba, inda ake sa-ran kamfanin zai yi hasarar kudin shiga kimanin naira biliyan 4.62 sakamakon wannan shirin.
Wani ma’aikacin NNPC a gidan man Obasanjo Way dake birnin Abuja, ya tabbatar da cewa, dole sai ta manhajar waya ce kawai za a iya samun farashin mai rahusa.
Ya ci-gaba da cewa, idan mutum ya sauke manhajar NNPCL a wayarsa ta salula, litar man da ake siyarwa a gidan mai kan naira 1,405, za a siyar masa shi kan naira 1,339.