NE

News Elementor

Ƙungiyar ƙabilu mazauna jihar Sokoto sun bi Ubandoma zuwa APC

Ƙungiyar ƙabilu mazauna Jihar Sokoto ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar ADC, suna masu bayyana rashin gamsuwa da shugabancin jam’iyyar da kuma wasu daga cikin matakan da ta ɗauka.

Shugaban ƙungiyar, Kwamared Raymond Ugbe Agba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar, inda ya ce ƙungiyar ta janye duk wani goyon baya da take bai wa jam’iyyar a jihar.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan abin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin ware Mallam Sa’idu Umar Ubandoma daga samun tikitin takarar gwamna, duk da irin gudunmawar da ta ce ya bayar wajen gina jam’iyyar ta hanyar wayar da kan jama’a da ƙarfafa ta daga matakin ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ta rasa amincewa da shugabancin jam’iyyar, tana zargin cewa wasu tsiraru na fifita muradunsu fiye da ra’ayin mafi yawan mambobi da magoya baya, tare da yin watsi da ƙwazo, sadaukarwa da biyayya.

Ta ce ficewarta daga jam’iyyar ta fara aiki tun daga ranar 24 ga Mayu, 2026, inda ta dakatar da duk wani aiki da goyon baya ga ADC a Jihar Sokoto.

Sun kuma tabbatar da ci gaba da biyayya ga Mallam Sa’idu Umar Ubandoma, tare da alƙawarin mara masa baya a duk wata tafiyar siyasa da zai zaɓa a gaba.

Daraktan Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Simon Kumden, ya ce ba za su iya ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar ADC ba, wadda a cewarsa, ke fifita muradun wasu tsiraru a kan ra’ayin jama’a ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM