NE

News Elementor

Ya kamata ƴan adawa su haɗa kai ƙarƙashin Peter Obi a zaɓen 2027– Aisha Yesufu

Fitacciyar mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Aisha Yesufu, ta buƙaci jam’iyyun adawa a Najeriya da su haɗa kai a ƙarƙashin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Yesufu ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce yin hakan ba yana nufin jam’iyyun siyasar za su rushe ko su mika wuya ba.

Ta ce ba jam’iyyar da ke da mafi yawan masu hayaniya a kafafen sada zumunta ce za ta lashe zaɓen 2027 ba, sai wadda ta iya haɗa ƙarfinta wuri guda.

Ta kuma jaddada cewa Peter Obi ba ɗan takarar wata jam’iyya guda kaɗai ba ne, illa ɗan takarar da ke da mafi kyawun tarihin aiki a cikin waɗanda za su fafata.

A cewarta, an ayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 da kashi 36 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da sauran ƙuri’un suka tafi ga jam’iyyun adawa.

Ta yi kira ga jam’iyyun adawa da su kafa ƙawance mai ƙarfi domin tunkarar zaɓen 2027, tana mai cewa matsalar ba ta taɓa kasancewa a lissafin ƙuri’u ba, domin alkaluman suna ci gaba da nuna cewa adawa na da damar samun rinjaye idan ta haɗa kai.

Har ila yau, tsohuwar jagorar ƙungiyar BringBackOurGirls, ta nuna damuwarta kan yadda jam’iyyun adawa ke ci gaba da rarrabuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM