NE

News Elementor

Ƙungiyar kula da lamurran Musulmi ta Najeriya, MPAC, ta soki gwamnatin tarayya bisa rashin ambaton Falasɗinu a jawabin da ta gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ƙungiyar ta ce a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na baya, Najeriya ta yi tsokaci sosai kan halin da ake ciki a Gaza, amma a taron na wannan shekarar, ƙasar ta kasa ambaton Falasɗinu, al’ummar ƙasar da kuma batun kafa ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.


A cikin wata sanarwa da Daraktan Zartarwa na MPAC, Disu Kamor, ya fitar, ƙungiyar ta ce jawabin da Najeriya ta gabatar a wannan karon ya fi mayar da hankali ne kan sauye-sauyen da ake son yi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, samar da kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, fasahar basirar ɗan Adam, basussuka da kuma yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel.


Sai dai MPAC ta ce duk da cewa jawabin Najeriya yana da shafuka 24, bai ƙunshi wani bayani kan Falasɗinu ba.


Ƙungiyar ta ce wannan mataki ya saba da matsayin da Najeriya ta nuna a taron UNGA na 80, inda ta yi magana kan abin da ta bayyana a matsayin musgunawa fararen hula a Gaza da kuma buƙatar kafa ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.


A cewar ƙungiyar, sauyin matsayar Najeriya a wannan karon ya haifar da tambayoyi kan yadda ƙasar ke kallon batun Falasɗinu da kuma matsayinta a kan rikicin Gaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM