Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na fuskantar sakamakon abin da ya kira rashin kyakkyawan shugabanci a lokacin da yake mulki.
Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya mayar da martani kan korafin El-Rufai cewa wasu daga cikin abokansa da makusantansa sun yi watsi da shi yayin da yake fuskantar matsaloli.
Ya zargi gwamnatin El-Rufai da rashin mutunta doka, kamu tare da tsare masu suka da kuma amfani da ikon gwamnati wajen tursasa abokan hamayya tsakanin 2015 zuwa 2023.
Sani ya kawo misalan wasu mutane da ya ce an tsare su a zamanin El-Rufai, ciki har da ɗan jarida Luka Binyat, wasu shugabannin al’umma daga Kachia da malamai.
Ya kuma zargi gwamnatin El-Rufai da rashin daukar isassun matakan dakile hare-haren ’yan bindiga da ta’addanci a Kudancin Kaduna.
Sai dai El-Rufai bai mayar da martani kan zarge-zargen ba.