Kungiyar Likitocin masu neman ƙwarewa ta ƙasa (NARD) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu da ta cika wasu buƙatunta da suka shafi walwala da ci gaban sana’ar likitocin.
NARD ta bayar da wa’adin ne a yayin taronta na shekara-shekara karo na 46 da aka gudanar a ranar Lahadi a Calabar, Jihar Cross River.
Kungiyar ta yi gargadin cewa idan gwamnati ta gaza warware matsalolin da take fuskanta, hakan na iya haifar da ɗaukar matakin yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Ogar Emmanuel Idoko, wanda ya karanta ƙudurin taron, ya ce NARD na damuwa da jinkirin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tsakaninta da gwamnatin tarayya.
Ya ce jinkirin ya daɗe fiye da yadda za a amince da shi.
Daga cikin buƙatun da ƙungiyar ta gabatar akwai batutuwan albashi da alawus-alawus, ci gaban aiki, yawan nauyin aiki, ƙarancin ma’aikata da kuma inganta walwalar likitocin.
NARD ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, musamman waɗanda suka shafi inganta yanayin aiki da ci gaban ƙwarewar likitoci.
Kungiyar ta kuma ce gwamnatin ta kammala nazarin tsarin albashi da sauran kuɗaɗen ƙwararru na likitoci, tana mai cewa tsarin da ake amfani da shi yanzu bai ƙara dacewa da yanayin tattalin arzikin ƙasar ba.
NARD ta nemi a samar da cikakken tsarin biyan diyya ga likitocin da ke gudanar da ƙarin aiki sakamakon ƙarancin ma’aikata a asibitoci.
Ta kuma buƙaci samar da bayanai sahihai da za su tabbatar da biyan likitocin da ke gudanar da ayyukan da suka wuce nauyin da aka ɗora musu.
Haka kuma, kungiyar ta nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa ma’aikatan lafiya, inda ta yi kira da a aiwatar da manufofi da matakan kariya daga hare-hare a asibitoci.
NARD ta kuma nuna damuwa kan ci gaba da ƙaura da likitoci da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya ke yi daga Najeriya.
Ta buƙaci Ma’aikatar Lafiya da Jinƙai ta Tarayya ta gaggauta magance abubuwan da ke haddasa ƙaurar ƙwararrun ma’aikatan lafiya zuwa ƙasashen waje.
Haka kuma, kungiyar ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su ba da fifiko ga walwalar likitoci da sauran ma’aikatan lafiya da ke aiki a cibiyoyinsu tare da tabbatar da aiwatar da manufofin walwala da suka dace.