NE

News Elementor

Gwamnatin tarayya ta nemi haɗin kai daga ƙasashen Duniya domin daƙile matsalar ta’addanci

Ministan Tsaro ya nemi haɗin kan duniya wajen yaƙi da ta’addanci a samun haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya domin tunkarar ta’addanci, satar ɗanyen mai, laifukan intanet da sauran matsalolin da ke barazana ga tsaron Najeriya.

Musa ya yi wannan kira ne a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da ke gudana a birnin New York, inda ya ce ya kamata haɗin gwiwar ya ƙunshi gwamnati, al’umma, ƙasashen duniya masu ƙawance da kuma kamfanoni masu zaman kansu.


A cewarsa, matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta suna da sarkakiya sosai, har ta kai ga ba za a iya magance su ta hanyar wata hukuma ko ƙasa guda ɗaya ba.

Ministan ya ce duk da cewa sojoji da sauran jami’an tsaro ne ke kan gaba wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, ba za a iya samar da ɗorewar zaman lafiya ta hanyar matakan soji kaɗai ba.


Saboda haka, Musa ya ce Najeriya na buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa da Majalisar Ɗinkin Duniya, Tarayyar Afirka, ECOWAS, ƙasashen abokan hulɗa, ƙungiyoyin fararen hula, masu bincike da kamfanoni masu zaman kansu domin ƙara inganta hanyoyin magance matsalolin tsaro.

Ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen samar da cikakkiyar hanyar tunkarar barazanar tsaro tare da ƙarfafa ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM