NE

News Elementor

Ƙungiyar masu sayar da taba sigari ta yi alƙawarin baiwa gwamnatin Kano haɗin-kai don cigaban kasuwancin su

Ƙungiyar Masu Sayar da Sigari ta Jihar Kano ta yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye ta Jihar Kano (KCPC), domin tabbatar da bin dokoki da ƙa’idojin da suka shafi sayar da sigari ga jama’a.

Da ya ke jawabi a yayin wata ganawa da hukumar ta KCPC, Shugaban ƙungiyar na jihar, Alhaji Ayuba Goza, ya ce dukkan ƙa’idoji da dokokin da su ka shafi sayar da sigari an bayyana su a fili a jikin kwalayen sigarin.

Sai dai ya bayyana cewa, a wasu lokuta ƙungiyar na fuskantar ƙalubalen jinkirin jigilar sigari da kuma isar da shi daga hannun masu kawo musu kaya, lamarin da kan iya haifar da wasu matsaloli lokaci zuwa lokaci.

A wata sanarwa da kakakin KCPC, Jamilu Mustapha Yakasai ya fitar a ranar Juma’a a Kano, Goza ya yi alkawarin yin aiki tare da mambobin ƙungiyar domin tabbatar da ci gaba da bin dukkan dokoki da ƙa’idojin da suka shafi sayar da sigari.

A nasa jawabin, shugaban KCPC, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ya bayyana cewa doka ta haramta sayar da sigari ga mutanen da shekarunsu ba su kai 18 ba.

Ya kuma jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a game da illolin shan sigari ga lafiya, tare da tabbatar da bin ƙa’idojin da suka shafi bayanan da ake sanyawa a jikin kwalayen sigari, ciki har da ranar ƙarewar amfani da shi.

Dr. Ibrahim ya gode wa shugabannin ƙungiyar bisa amincewarsu da gayyatar da hukumar ta yi musu, tare da tabbatar musu da cewa KCPC za ta ci gaba da sa ido kan yadda ake sayar da sigari a faɗin Jihar Kano, domin tabbatar da bin doka da kuma kare lafiya da jin daɗin al’ummar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM