NE

News Elementor

Amurka za ta aika wa Najeriya kayan aikin soja domin yaƙi da ta’addanci

Amurka ta ce za ta aika wa Najeriya wasu kayan aikin soja, yayin da ƙasashen biyu ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro domin yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da sauran barazanar tsaro.


Rundunar sojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka, AFRICOM, ta bayyana cewa wani jirgin saman sojin saman Amurka kirar C-17 zai kawo kayan aikin ga Rundunar Sojin Saman Najeriya a ƙarshen wannan mako.


A cewar AFRICOM, kayan aikin na cikin yarjejeniyar sayar da kayayyakin soja tsakanin Amurka da Najeriya, wadda ake ganin za ta ƙara ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin ƙasashen biyu tare da taimakawa Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci.


Isar da kayan aikin na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, ’yan bindiga da sauran masu haddasa rashin tsaro a sassan ƙasar.


Duk da cewa rundunar sojin Najeriya ta samu wasu nasarori a ayyukan da ta gudanar a watannin baya-bayan nan, hare-haren ’yan bindiga da sace mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da faruwa a wasu yankuna.


Najeriya da Amurka sun kuma ƙara haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri, horas da jami’an tsaro da kuma samar da kayan tallafin soja, domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM