
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ce jihar Kano na da muhimmanci wajen samun nasar jam’iyyar ADC a Nijeriya.
Atiku ya baiyana hakan ne a Abuja yayin da ya shirya buɗe-baki ga wani ƙusa a jam’iyyar ADC a jihar Kano, Ambasada Saminu Isyaku Kura.
A yayin ziyarar, Atiku, mai neman kujerar shugaban ƙasa a ADC, ya ci alwashin cigaba da mara wa jam’iyyar baya tare da bunƙasa ta karkashin jagorancin matasa masu kishin ƙasa.
Atiku ya kuma yi nazari kan yadda matasan jam’iyyar ke gudanar da ayyukansu ba dare ba rana domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓukan da ke tafe, musamman s jihar Kano.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yaba da ƙwazon matasan jam’iyyar tare da jinjinawa rawar da Amb. S.A Saminu Shehi Kura ke takawa wajen ƙarfafa gwiwar matasa da kuma gina tubalin nasarar jam’iyyar a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
A nasa jawabin, Saminu Kura ya yi alkawarin ci gaba da hidimtawa jam’iyyar tare da aiki da matasa don ganin ta kai gaci a zabukan 2027.