NE

News Elementor

Gwamnatin Jihar Legas ta Kama Mutane 46 Saboda Yin Ba+haya a Fili

Gwamnatin Jihar Legas ta ƙara ƙarfafa hukunta masu yin bahaya a fili, inda ta kama mutane 46 a sabon aikin sintiri da aka gudanarwa a manyan titunan kasuwanci na Tsibirin Legas.

Hukumar ta aiwatar da kamun ne ta hanyar rundunar yaƙi da yin bayan gida a Fili ta Jihar Legas a safiyar wannan makon, inda aka mayar da hankali kan wuraren da aka gano rashin tsaftar muhalli, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na aiwatar da dokokin muhalli da kare lafiyar jama’a.

Daraktan gudanarwa kuma shugaban hukumar Kula da shara ta Legas, Dr. Muyiwa Gbadegesin, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin hukuma na gwamnatin jihar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Jihar Legas, ta hanyar Rundunar Yaki da Yin Bayan Gida a Fili, ta kama maza da mata 46 masu laifi a yayin wani aikin sintiri da aka tsara da aka gudanar a safiyar yau a fadin Tsibirin Legas.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM