NE

News Elementor

Jam’iyyar ADC Ta Kaddamar Da Shirin Rajistar Mambobi Da Sabunta Rajista, Tare Da Fitar Da Ranakun Manyan Taroka Na Kasa A 2026.

Jam’iyyar ADC ta fara shirin aikin rajistar sabbin mambobi da sabunta rajista ga mambobinta na tsawon kwana 90 a faɗin ƙasar nan.

Wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Asabar, ta ce wannan mataki ya biyo bayan kammala taron kwamitin gudanarwar jam’iyar na ƙasa da aka yi a ranar 27 ga Nuwamba, 2025.

Jam’iyyar ta kuma bayyana ranakun wucin gadi na gudanar da tarukan jam’iyya da zaɓen wakilai a matakan rumfar zaɓe, mazabu da kuma ƙananan hukumomi.

A cewar wata wasiƙa daga Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola, za a gudanar da tarukan tsakanin 20 zuwa 27 ga Janairu, 2026, kafin a kammala da babban taron ƙasa mara zaɓe a Faburairu 2026 a Abuja.

Jam’iyyar ta ce wannan shiri na da muhimmanci wajen ƙarfafa jam’iyyar da tsarin gudanarwarta a faɗin ƙasa, tare da jaddada bin doka, gda dimokiraɗiyyar a fadin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM