Tsohon dan wasan gaba na Najeriya, Ahmed Musa, ya sanar da yin murabus daga Super Eagles, bayan shafe shekaru 15 a fagen wasa na kasa da kasa.
Musa, mai shekaru 31, ya fara wakiltar Najeriya a shekarar 2010 kuma ya zama daya daga cikin shahararrun ‘yan wasan gaba na kasa. A tsawon shekaru, ya wakilci Super Eagles a gasar FIFA World Cup sau uku (2010, 2014, 2018) da kuma gasar Afrika Cup of Nations sau da yawa, inda ya ci kwallaye masu muhimmanci kuma ya samu yabo saboda fasaha, sauri, da jajircewarsa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Musa ya nuna godiya ga abokan wasa, masu horaswa, da magoya bayan Najeriya, inda ya ce: “Ya kasan ce abun mamaki na sanya kayan kasa. Ina alfahari da kowane lokaci da na yi ina wakiltar kasata, kuma zan ci gaba da goyon bayan kwallon Najeriya a kowane hali.”
Yin murabus dinsa na nuna ƙarshen wani zamani ga kwallon kafa ta Najeriya, yayin da Musa ya bar tarihi a matsayin daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi kowa ci kwallaye a kasa da kasa kuma wanda ya kasance abin koyi ga matasa masu tasowa.