A makon da ya gabata ne mai horar da ƴanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya Éric Sékou Chelle ya fitar da sunayen ƴan ƙwallo 28 waɗanda za su wakilci ƙasar a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025.
Kocin zai je gasar, wadda za a buga a ƙasar Morocco ne da zimmar samun nasara gagaruma bayan an yi waje da Najeriya a wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026.
Wasu fitattu yan wasa da basa cikin tawagar sun hada da Ahmed Musa, Umar Sadiq, Maduka Emilio Okoye, Alhassan Yusuf, Ola Aina, Victor Boniface, Terem Moffi da dai sauran su.
Daga cikin ƴan ƙwallon da Chelle ya fitar, akwai guda biyar da ba su taɓa wakiltar Najeriya a babbar tawaga ba, lamarin da ya janyo cece-kuce, a gefe ɗaya kuma wasu suke yaba masa da fito da sabbin ƴanwasa.
Sabbin ƴan wasa biyar ɗin su ne ɗan wasan baya Ryan Alebiosu da ɗan wasan tsakiya Ebenezer Akinsanmiro da Usman Muhammed da Tochukwu Nnadi waɗanda su ma duk ƴanwasan tsakiya ne, sai ɗan wasan gaba, Salim Fago Lawal.
Najeriya za ta buga wasanta na farko ne da kasar Tanzaniya a ranar 23 ga Disamba.