Har yanzu gidajen man fetur a Nigeria ba su rage farashi ba, duk da sabon farashin naira 739 ko kuma 740 da matatar Dangote ta sanar.
Manema labarai dake bibiyar yanayin farashin litar mai sun gano cewa, gidajen man fetur na MRS a jihar Legas da kewaye na siyar da litar mai kan naira 850, kwatankwachin Karin naira 110 kan farashin da Aliko Dangote ya sanar.
Dangote dai ya tabbatarwa yan Nigeria cewa, dukkanin gidajen man fetur na MRS za su rinka siyar da litar mai akan naira 739 zuwa 740.
To saidai, gidan man fetur na MRS dake Alagbole a tsakanin jihar Legas da Ogun, ana siyar da man ne kan naira 850. Kazalika an lura da wani gidan man MRS dake kan titin Ekoro, inda ake siyar da litar man fetur kan naira 825 zuwa 870.
A makon da ya gabata, kungiyar IPMAN ta bukaci wakillanta da su rinka siyen mai daga matatar Dangote saboda yana siyar da man da arha kuma zai fara jigilar man feturin kyauta a watan Junairu mai zuwa.