Amurika ta kulla wata yarjejeniya da Nigeria domin karfafa tsarin kiwon lafiya, musamman ga Mabiya addinin kirista.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurika tare da majalisar dokokin kasar za su kashe kusan dala biliyan 2.1 domin samar da magungunan cutar HIV, da tarin TB, da malaria, da polio da kuma kula d alafiyar mata da kananna yara.
A karkashin sabuwar yarjejeniyar da aka kulla a jiya Assabar, gwamnatin Nigeria za ta kara yawan kudin da take kashewa a bangaren lafiya da kusan dala biliyan 3 a tsawon shekaru 5 na yarjejeiyar.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurika, Thomas Pigott ya ce wannan ce yarjejeniya mafi girma da Amurika ta kulla da wata kasa tun bayan kaddamar da shirin America ce farko.
Yarjejeniyar ta shafi yin suaye-sauye a matakan kiwon lafiya da Nigeria ke dauka domin kare Mabiya addinin kirista daga fuskantar matsaloli.