Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da cewa daga ranar 11 zuwa 14 ga watan Fabrairu ne za a gudanar da bikin kamun kifi na ƙasa da ƙasa na Argungu.
Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da ’yan jarida bayan wani taro na musamman da Kwamitin Babban Bikin Jiha da Kwamitin Shirya Biki na Masarautar Argungu suka gudanar.
Taron ya gudana ne a ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi shirye-shiryen bikin.
Sarkin ya bayyana cewa bikin kamun kifin na Argungu ya samo asali ne a matsayin wani yunƙuri na samar da zaman lafiya tsakanin mayaƙan Daular Sakkwato da Masarautar Kanta.
Ya ce saboda muhimmancin tarihinsa, daga bisani UNESCO ta amince da bikin a matsayin bikin al’adu na ƙasa da ƙasa.
Sarki ya ƙara da cewa bayan Yaƙin Basasar Najeriya, an kuma yi amfani da bikin wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
A cewarsa, bikin ya haɗa masunta daga sassa daban-daban na ƙasar nan a zamanin mulkin Janar Yakubu Gowon domin nuna alamar haɗin kai da zaman lafiya. Ya bayyana cewa ana sa ran bikin na bana zai jawo manyan baƙi daga sassa daban-daban na duniya tare da nuna al’adun Masarautar Argungu ga duniya baki ɗaya.
Da yake jawabi a taron, Shugaban Kwamitin Babban Bikin na Jiha kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, ya ce shirye-shirye sun yi nisa. Ya ce an kafa ƙananan kwamitoci daban-daban domin tabbatar da nasarar bikin, inda ya ƙara da cewa gwamnati ta tanadi dukkan muhimman abubuwa kamar shirya wajen taro, karɓar baƙi, kayayyakin aiki da kuma kyaututtuka ga waɗanda suka yi nasara.