
An tsaurara tsaro a gidan gwamnatin Jihar Kano a ranar Litinin, biyo bayan rahotannin da ke nuni da shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ficewa daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC.
Jaridar Daily Trust ta lura da tarin jami’an tsaro daga rundunar ‘yansandan Najeriya da kuma hukumar tsaron farin kaya (DSS) a babbar kofar shiga gidan gwamnatin.
Duk da cewa ba a tabbatar da shirin ficewar a hukumance ba, ana bayanai na nuni da cewa gwamnan zai sauya sheka daga yanzu zuwa kowanne lokaci.
Wakilin jaridar Daily Trust ya lura cewa akalla motocin tsaro masu sulke na ‘yansanda da DSS sun kasance a muhimman wurare, ciki har da babbar kofar shiga da kuma zagayen hanya da ke kaiwa gidan gwamnatin.