
Fashewar ta lalata wata tirela da ke ɗauke da siminti a kusa da ƙauyen Unguwar Mai Chida, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa sosai.
Majiyoyi a yankin sun ce ana zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa na’urar, wadda ta fashe a lokacin da motar ke wucewa ta yankin.
Motar dakon, na kan hanyarta daga Sokoto zuwa Kaduna.