NE

News Elementor

An Kammala Taron Kasuwanci Na Duniya Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba

An kammala taron kasuwanci na duniya da hukumar WTO ta shirya a birnin Yaounde na ƙasar Kamaru ba tare da cimma matsayar bai ɗaya ba, game da samar da yarjejeniyar kasuwanci da dukkan ƙasashe za su amince da ita.

Bayan share kwanaki huɗu ana gudanar da taron kasuwanci da ya haɗa ministocin ƙasashe da dama a birnin Yaounde, mahalarta taron sun gaza cimma matsayar bai ɗaya.

Yunƙurin samar da yarjejeniyar kasuwanci da illahirin ƙasashen za su amince da ita, shi ne muhimmin batun da ministocin kasuwanci daga sassa daban daban na duniya suka share tsawon kwanaki suna tattaunawa a kai.

To sai dai irin yadda shugaban Amurka Donald Trump ya sa ƙafa ya yi fatali da yarjeniyoyin kasuwancin da Washington ta rattaba wa hannu a baya shi ne ya fi ɗaukar hankali a taron.

Dama dai anyi tsammanin a gaza samun matsayar bai ɗaya tun gabanin fara tattaunawar, kodayake anyi tunanin aƙalla za a amince da sabunta yarjejeniyar kasuwancin.

A ƙarshe dai, duk da rashin amincewa da ƙasar Brazil ta nuna, ministocin kasuwancin sun ƙi amincewa da tsawaita yarjejeniyar zuwa fiye da shekaru biyu, matakin da Amurka ke adawa da shi.

Masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci sun bayyana matuƙar damuwa game da halin da aka ƙarƙare taron, sun mai cewa rashin cimma marsayar zai haifar da gagarumin koma baya ga kasuwanci, a wani yanayi da rikice-rikice suka sake jefa tattalin arziƙi duniya cikin yanayin rashin tabbas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM