NE

News Elementor

Gwamnatin Tarayya Ta ce Mutum Miliyan 9.2 Suka Amfana Da Tallafin Naira 25,000 A Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce magidanta miliyan 9.2 ne suka amfana da shirin bada tallafin kudi domin yaki da talauci.

Shirin, wanda ke gudana karkashin kudurin Sabunta Fata na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya samu karbuwa sosai a tsakanin magidanta masu karamin karfi a fadin Nigeria.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce yanzu haka gwamnatin tarayya na fatan tallafawa wasu karin magidanta miliyan 15 a karkashin shirin.

Da yake zantawa a taron manema labarai a Abuja, ministan jinkai da rage fatara, Dr Nernard Doro, ya bayyana shirin a matsayin sauyi daga matakai masu garejen zango da gwamnati ke dauka zuwa tsarin bada tallafi na musamman.

A karkashin shirin dai, kowane magidanci zai samu naira 75,000 na tsawon wata uku, domin siyen abinci, kiwon lafiya da kuma ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM